1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kafa sabuwar gwamnati a kasar Czech

January 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuUw

A janhuriyar Czech, shugaba Vaclav Klaus ya amince da sabuwar gwamnatin hadaka a karkashin jagorancin prime minista, Mirek Topolanek, bayan watanni bakwai ana fama da rigingimu ,sakamakon zaben da ba´a idar ba a wannan kasa.

Gwamnatin Topolanek, data kunshi jammiyyun siyasa guda uku a wannan kasa na da kwanaki 30 ,na samun nasaran amincewar majalisar dokokin kasar.

A yanzu haka dai tana da kuriu 100, a wannan majalisa mai wakilai 200.

A watan satumban daya gabata ne dai, Mr Topolanek ya gaza a yunkurinsa na kafa gwamnati a janhuriyar ta Czech.