Kokarin kafa gwamnati a yankin Palasdinawa | Labarai | DW | 21.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin kafa gwamnati a yankin Palasdinawa

Shugaban yankin Palasdinawa, Mahmud Abbas yace zai bukaci faraministan da kungiyyar Hamas ta nada,wato Isma´il Haniyya daya kokarta kafa gwamnati ba tare da bata lokaci ba.

Duk da cewa kungiyyar Hamas ta masu kishin addinin Islama tace zata kafa gwamnatin hadaka ne, to amma da alama har yanzu an kasa cimma wata matsaya a tsakanin su da jamiyyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas.

A kuwa yayin da ake cikin wannan hali, kasar Israela ta kaddamar da wasu matakai na ganin wannan gwamnati da za´a kafa bata yi tasiri ba.

Daga cikin matakan kuwa akwai dakatar da mika kudaden haraji da take tarawa yankin ta hanyar shigi da fici na kayayyaki, da yawan su ya tasamma dalar Amurka miliyan 50 a kowa ne wata.

Har ilya yau, mahukuntan na Israela na kuma kara daukaka kira ga kasashen duniya dasu mayar da wannan gwamnati ta Hamas saniyar ware.

Kafin dai daukar wadannan matakai, a can baya Amurka tuni ta kira kungiyyar ta Hamas ta yan ta´adda a hannu daya kuma tare da dakatar da kudaden tallafi na raya kasa da take bawa yankin.