Kokarin horas da tsofin mayakan Boko Haram | Labarai | DW | 06.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin horas da tsofin mayakan Boko Haram

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da kafa wata cibiyar horas da tsofin mayakan Boko Haramwadanda suka mika wuya domin su samu dogaro da Kai.

Wannan cibiya dai, da ba a bayyana inda aka kafata ba, za ta mayar da hankali ne wajan koya wa tsofin mayakan kungiyar aiyyukan hannu domin samun dogaro da kai, tare da fadakar da su ta yadda hankalinsu zai dawo ga rayuwa ta yau da kullun cikin al'umma. Rundunar sojojin na Najeriya dai ta ce, dakarunta za su ci-gaba da yakar 'yan kungiyar da ba su mika kansu ba.

A makon da ya gabata ne dai kungiyar ta Boko Haram cikin wani sabon bidiyo ta sanar cewa za ta ci-gaba da gudanar da aiyyukanta na kai hare-hare bisa umarnin shugabansu Abubakar Shekau wanda shi ma bisa dukkannin alamu ke fama da tarin matsaloli na rayuwa.