Kokarin hana shigar yan gudun hijira turai ta kwale kwale | Labarai | DW | 28.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin hana shigar yan gudun hijira turai ta kwale kwale

Ministocin harkokin wajen Kungiyar Taraiyar Turai da na kasashen larabawa da kuma arewacin Afrika suna shirin kara tattaunawa a kasar Finland kan matasalar yan gudun hijira dake kokarin shiga turai da kananan kwale kwale.

A karshen makon daya gabata ne dai wani kwale kwale dauke da yan gudun hijira dake kokarin isa tsibirin Canary na kasa Spain ya nutse cikin teku a yammacin sahjara inda akalla mutane 10 suka halaka.

Wajen taron na Finland ministocin kasashen Malta da Spain da Italy zasu nemo matakan daya kamata a dauka domin kawo karshen wannan matsala.

Bada jimanan nan bane dai Spain ta sanya hannu kan yarjejeniyar hadin kai da wasu kasashen Afrika,wadanda suka hada da Moroko,da Senegal da kuma Libya tare da nufin musayar bayanai kann fataucin mutane da kuma baiwa yan sanda Afrika horo.

A wannan shekara kadai yan gudun hijira 28,000 suka shiga tsibirin Canary.