Kokarin hana kera bom mai dauke da kwanso a cikin sa | Labarai | DW | 23.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin hana kera bom mai dauke da kwanso a cikin sa

Nan gaba kadan a kasar Norway, za a fara gudanar da wani taro kann daukar matakin hana kera bon, dake dauke da kwanson bama bamai a cikin sa.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa irin wadannan bama bamai masu kwansun wasu bama baman a cikin su, na haifar da illa babba ga rayuwar fararen hula ga duk inda aka jefa shi.

Ya zuwa yanzu dai kasashe irin su Amurka da Russia da kuma China na adawa da shirin hana kera irin wadannan bama bamai.

Bayanai dai sun rawaito mahukuntan na Norway na cin alwashin ganin, an samu matsaya guda a game da kokari kawo karshen kera irin wadannan muggan bama bamai.

Za dai a shafe kwanaki biyu, ana gudanar da wannan taro a birnin Oslo na kasar ta Norway. Wakilan kasashe 48 daga kasashe daban daban na duniya ne, ake sa ran zasu halarci wannan taro.