Kokarin dakile yaduwar murar tsuntsaye a nahiyar Turai | Labarai | DW | 16.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin dakile yaduwar murar tsuntsaye a nahiyar Turai

Bisa yadda cutar murar tsuntsaye ke ci gaba da yaduwa a kasashe daban daban na duniya, wasu daga cikin gwamnatocin kasashen turai na ci gaba da daukar matakan rigakafi, wanda hausawa kance yafi magani.

Daga cikin wadannan matakai dai akwai killace tsuntsayen gida da kuma dabbobi, a hannu daya kuma da kwantarwa da mutane hankali.

Daukar wadannan matakai dai ya biyo bayan gargadin da kungiyyar gamayyar turai wato Eu tayi ne cewa, wannan cuta ka iya bulla a wasu kasashe bisa irin zirga zirgar tsuntsaye na daji daga kasa izuwa kasa.

Tarayyar Jamus dai ta kasance, kasa ta baya bayan nan data samu bullar cutar ta murar tsuntsaye mai nau´in H5N1.

Ba a da bayan kasar ta Jamus, akwai kasashe irin su Bulgeriya da Greece da Italiya da Romania da kuma wasu bangarori na Eu dake kasar Russia.