Kokarin dakile yaduwar cutar AIDS ko SIDA | Zamantakewa | DW | 01.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kokarin dakile yaduwar cutar AIDS ko SIDA

A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar yaki da cutar AIDS ko kuma SIDA da Majalisar Dinkin Duniya ta ware, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fito da wata sabuwar hanyar gwajin cutar cikin sirri.

Welt-Aids-Tag 2016 (Reuters/Str.)

Sabuawar hanyar gwajin cutar HIV/AIDs ko SIDA

A cewar sabon rahoton da Hukumar Lafiya ta Duniyar WHO ta fitar rashin sanin hakikanin masu dauke da cutar me karya garkuwar jiki, na zama abin da ke hanawa hukumar rawar gaban hansti a yunkurin kawar da cutar a tsakanin al'umma. To sai dai rahoton ya nunar da cewa mutane miliyan 18 da ke fama da cutar a fadin duniya, na sane da cutar a jikinsu amma kaso mafi tsoka basa samun tallafin jinya na musamman. Wannan ya sa kaso 40 cikin dari na masu dauke da cutar basu san matsayin jininsu ba.

Wannan ya sa DW ta tambayai Dr. Gregoyr Haltl, kakakin Hukumar Lafiya ta Duniyar WHO, kan yadda dabarun gwaji da suka bullo da shi zai taimaka a yaki da kwayar cutar. A cewarsa suna da yakinin cewa akwai mutane miliyan 14 da ba su san matsayinsu ba, wannan ya sa suka samar da sababbin dabarun gwaji da kai, da zai taimaka a gano in ana dauke da cutar mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS ko SIDA,  kazalika hakan zai ba su damar tsawon rayuwa dama kariya ga masu cutar a yayin jima'i. Wannan na'urar gwaji da kai, za ta bawa mutane damar amfani da wani bututu da za su hura iska ta baki ko ma gwajin jini ta hanyar huda tambarin yatsa dan gwada jinin a cikin sirri, da zai samar da sakamako cikin mintuna 20 kacal. To sai dai Dr. Gregoyr Haltl kakakin hukumar lafiya ta duniyan ya ce:

Südafrika Welt-Aids-Tag 2016 (Getty Images/AFP/M. Safodien )

Samar da allurar rigakafin cutar HIV/AIDs ko SIDA

"Na'urar na da tabbas, amma dai akwai bukatar garzayawa cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa bayan sanin sakamakon da ya nuna mutum na dauke da cutar. Babban abin da ke gabanmu shi ne jan hankalin hukumomi da gwamnatoci, da su aza kaimi domin samar da na'urar ga jama'a dan taimaka wa masu zama da cutar ba tare da sun sani ba."

A cikin shekaru 12 da suka gabata, an samu ci gaba da kimanin kso 48 cikin 100 na mutanen da suke zuwa gwajin jini domin tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar ta HIV/AIDS ko SIDA da ke karya garkuwar jiki. Kididdiga dai ta nunar da cewa kaso 40 cikin 100 da  na masu dauke da cutar sun kasance masu auren jinsi guda, da mata masu zaman kansu da fursunoni da kuma jariran da akan haifa suna dauke da ita. Sai dai jariran da aka haifa a wannan shekara, na wakilatar jimillar mutane sama da miliyan guda da har yanzu ba su da tabbacin matsayinsu dangane da wannan cuta. Wannan ya sa WHO ke ganin sabon tsarin gwaji da kai, zai yi tasiri a kasahen Afirka da ke Kudu da sahara inda nan ne cutar tafi kamari a duk fadin duniya.

Kasashen Afirka uku ne dai hukumar ta WHO za ta tallafawa don samar da na'urorin gwajin baya ga sauran kasashe 27 da zummar dakile yaduwar kwayar cutar ta  HIV/AIDs ko kuma SIDA nan da shekaru 14 masu zuwa. Sai dai tuni Afirka ta kudu ta kaddamar da gagarumin shirin gwajin wata allurar rigakafin kamuwa da kwayar cutar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin