Kokarin da ake na warware rikicin yankin gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 15.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin da ake na warware rikicin yankin gabas ta tsakiya

Sarki Abdallah na Jordan ya bukaci kasar Amurka data dawo da daftarin zaman lafiyar nan, na yankin gabas ta tsakiya cikin hayyacin sa.

Rashin daukar wannan mataki, a cewar Sarkin na Jordan abune da ka iya kara haifar da karuwar rikice rikice da tashe tashen hankula a yankin baki daya.

Sarkin na Jordan ya daukaka wannan kiran ne ga sakatariyar harkokin wajen kasar Amurkan,wato CR, wacce ta kai ziyara izuwa kasar.

Kafin dai isar ta izuwa kasar ta Jordan, CR ta gana da shugaba Mahmud Abbas na yankin Palasdinawa, a game da kokarin da ake na samo bakin zaren warware rikicin dake tsakanin Israela da Palasdinawa.

Kafin dai kammala wannan ziyara da take a yankin gabas ta tsakiyar, ana sa ran CR za kuma ta gana da Mr Ehud Olmert na Israela da kuma Hosni Mubarak na Masar.