Kokarin Amurka na shawo kan rikicin yankin Darfur | Labarai | DW | 09.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin Amurka na shawo kan rikicin yankin Darfur

Amurka ta rabawa mambobin kwamitin sulhu na Mdd kwafin wani daftari dake kunshe da bukatar Majalisar ta karbi ragamar tafiyar da aiyukan tsaro a yankin Darfur na Kasar Sudan.

Bugu da kari, daftarin ya kuma bukaci dawo da bataliyar sojin na Mdd dake kudancin kasar ta Sudan izuwa yankin na Darfur.

Daukar wannan mataki dai yazo ne awowi kadan , bayan shugaba Bush ya bayyana cewa zai gaggauta daukar matakin shawo kann rikicin na Yankin Darfur, a hannu daya kuma da taimakawa da abinci ga mutanen yankin.

Rahotanni dai sun nunar da cewa duk da kasancewar dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na kungiyyar Au dubu 7 ,

rikice rikice da tashe tashen hankula na ci gaba da yawaita ne a yankin na Darfur.