kofin kwallon kafa na duniya | Labarai | DW | 10.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kofin kwallon kafa na duniya

Kasar Italiya ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da ya gudana a nan Jamus inda ta doke Faransa da ci biyar da uku a bugu daga kai sai mai tsaron gida. Dubban jamaá a birnin Rome sun yi ta murna tare da kade kade da bushe bushe bisa nasarar ta kasar ta samu na daukar kofin duniyar a karo na hudu. Wanan dai shi ne karo na biyu a tarihin gasar cin kofin kwallon kafar ta duniya da aka kai ga bugun Penarity domin samun wanda zai lashe gasar. Dan wasan Faransa kuma kaftin din kungiyar Zinedin Zidane an fidda shi daga wasan a zagaye na biyu na karin lokaci bayan da ya yiwa dan wasan Italiya Marco Materazzi karo a kirji. Gasar ta karshe ya sami halartar shugaban kasar Italiya Giorgio Napolitano da kuma shugaban kasar Faransa Jacques Chirac.