Kofi Annan yayi taron manema labarai na karshe | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kofi Annan yayi taron manema labarai na karshe

Kofi Annan ya gudanar da taron manema labarai na karshe a matsayinsa na sakatare janar na MDD,inda ya baiyanawa manema labaran cewa zai ci gaba da aiki kann batutuwa da suke da muhimmanci a gareshi.

Ya kuma roki alummomin duniya da su gaggauta kawo karshen rikici a yankin darfur na kasar Sudan.

Annan yace abu mafi muni da ya taba faruwa a lokacin shugabancinsa shine yakin da Amurka ta jagoranta kann Iraqi da kuma batun rikici nan da ya ki ci yaki cinyewa game da batun mai don abinci a kasar ta Iraqi.