Kofi Annan yayi gargadi game da barkewar rikici a Chadi | Labarai | DW | 18.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kofi Annan yayi gargadi game da barkewar rikici a Chadi

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan,yayi gargadin cewa ci gaba da fada a kasar Chadi,inda yan tawaye suke kokarin hambarar da gwamnatin kasar,zai iya shafar yankin baki daya.

Kofi Annan ya fadawa manema labarai ce,ya kamata a kare yaduwar tashe tashen hankula a yankin,ya kuma baiyanawa taron komitin sulhu na majalisar rahotannin dake cewa da hannun kasar Sudan cikin rikicin na kasar Chadi,wanda yace muddin dai hakan ya tabbata bai kamata komitin yayi shiru akai ba.

Shugaba Idris Deby tuni dai ya zargi Sudan da laifin ingiza wannan tawaye akan gwamnatinsa,wadanda suka nemi yi masa juyin mulki a makon daya gabata.

A halin yanzu dai Idris deby ya bada tabbaci ga Majalisar Dinkin Duniya cewa,ba zai kori yan gudun hijira na Sudan su fiye da 200,000 da suke Chadi ba,kamar yadda yayi barazana a ranar jumaa bayan ya yanke huldar diplomasiya da gwamnatin Sudan.

Kofi Annan yace,ya tattauna da shugaban Kungiyar Taraiyar Afrika AU,Denis Sassou Nguesso na kasar Kongo,da kuma sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice game da yadda zaa magance rikicin Chadi da Sudan,wanda yace ya kamata kungiyar ta AU da sauran kasashen duniya su matsa masu lamba domin ganin cewa basu wuce gona da iri ba.