Kofi Annan ya lashi takobin ba da ƙaimi a fafutukar kyautata halin rayuwar al’umman Afirka. | Labarai | DW | 16.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kofi Annan ya lashi takobin ba da ƙaimi a fafutukar kyautata halin rayuwar al’umman Afirka.

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya mai barin gado, Kofi Annan, ya yi alkawarin ci gaba da aikinsa na fafutukar inganta halin rayuwar al’umman Afirka, bayan ya sauka daga muƙaminsa a ƙarshen wannan shekarar.

A ziyarar ban kwana da yake kai wa ƙasashen Afirka a muƙaminsa na babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniyar, Kofi Annan, ya ya da zango ne a birnin Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha, inda ya yi wa wani taro kan bunƙasa ayyukan raya ƙasa a nahiyar jawabi. A cikin jawabinsa Kofi Annan ya bayyana cewa, duk da saukar da zai yi daga muƙamin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniyar, hakan ba zai sa ya saduda ba, wajen ba da ƙaimi ga fafutukar da yake yi, na neman inganta halin rayuwar al’umman nahiyar Afirka. A yau ne kuma ake kyautata zaton cewa, Annan zai gana da shugabannin ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU a birnin na Addis Ababa, don tattauna batun samo bakin zaren warrware rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan.