Kofi Annan ya isa Bagadaza a wata ziyarar ba zata ga Iraki | Labarai | DW | 12.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kofi Annan ya isa Bagadaza a wata ziyarar ba zata ga Iraki

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya sauka a Bagadaza babban birnin Iraqi a wata ziyara ta ba zata. Wannan dai ita ce ziyarar sa ta farko zuwa Iraqi tun bayan da dakarun da Amirka kewa jagoranci suka kifar da gwamnatin Saddam Hussein a cikin shekara ta 2003. Annan ya gana da FM Ibrahim al-Jaafari da wasu shugabannin siyasar kasar, sannan ya yi kira ga al´umar kasar ta Iraqi da su dinke dukkan barakar dake tsakanin su. Annan ya goyi bayan kokarin da ake yi na sasanta dukkan al´umomin kasar. Ziyarar ta yi kicibis da barkewar sabbin tashe tashen hankula a babban birnin na Iraqi. ´Yan sanda sun ce akalla mutane 10 sun rasu sannan da dama sun samu raunuka a wani harin bam da mota da aka kai kan wata kasuwa dake kudu maso gabashin Bagadaza.