Kofi Annan ya ce Iran ta nuna sha´awar ci-gaba da shawarwari da EU | Labarai | DW | 13.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kofi Annan ya ce Iran ta nuna sha´awar ci-gaba da shawarwari da EU

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya ce Iran ta nuna shirin ci-gaba da tattaunawa da KTT akan shirin ta na nukiliya. Annan ya kara da cewa a na sa ganin yanzu lokaci bai yi ba da za´a mika wannan takaddama a gaban kwamitin sulhun MDD. Annan ya bayyana haka ne bayan hira ta wayar tarho da suka yi da babban mai shiga tsakani na Iran Ali Larijani. A jiya dai ne ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce tattauwar da ake yi tsakanin Iran da tarayyar Turai ta kai makura. Bayan wani taro a birnin Berlin ministan ya ce kasashe Jamus da Birtaniya da Faransa sun yi kira da a gudanar da wani taro na musamman na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wadda zata iya mika batun Iran din ga kwamitin sulhu don kakaba mata takunkumi. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice na goyon bayan wannan mataki. Ita ma a nana bangaren SGJ Angela Merkel cewa ta yi Iran ta wuce gona da iri. Gwamnatin Teheran dai ta yi biris da barazanar da ake yi na yin kararta a gaban kwamitin sulhu, inda a wannan mako ta fara aikin bincike a fannin nukiliya.