Kofi Annan ya baiyana bukatar samar da runduna mai karfi ta MDD don kiyaye zaman lafiya a Dafur. | Labarai | DW | 26.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kofi Annan ya baiyana bukatar samar da runduna mai karfi ta MDD don kiyaye zaman lafiya a Dafur.

Sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya bukaci samar da tawaga mai karfi ta dakarun kiyaye zaman lafiya a lardin Dafur na kasar Sudan . Kofi Annan yace a halin da ake ciki kungiyar gamaiyar Afrika na fama da karancin kudade na tafiyar da aikin dakarun kiyaye zaman lafiyar, Anan ya kara da cewa bisa ga tabarbarewar alámuran tsaro a yankin na Dafur dakarun na majalisar dinkin duniya na iya yin amfani da karfin tuwo domin kare rayukan jamaá. Sakataren majalaisar dinkin duniyar yace a halin da ake ciki akwai mutane fiye da miliyan biyu dake gudun hijira a yankin Dafur.