Kofi Anna ya bukaci karin kaimi wajen yaki da kananan makamai | Labarai | DW | 27.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kofi Anna ya bukaci karin kaimi wajen yaki da kananan makamai

Sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan yace wajibi ne kasashe su kara himma wajen kawar da kananan makamai daga hannun yan fasakwauri da kuma bata garin mutane. Annan ya yi wannan bayanin ne yayin da yake jawabi ga wani babban taro kann yadda zaá rage cinikin irin wadannan makamai ba bisa kaída ba. Sakataren majalisar dinkin duniya ya shaidawa mahalarta taron cewa an sami dan cigaba shekaru biyar da suka gabata, bayan da kasashen suka yi alkawarin yaki da yaduwar kananan makaman. Yace to amma an sami rauni daga bangaren kasashen na rashin inganta dokoki tare da karbewa da kuma lalata irin wadannan makamai. Yace majalisar dinkin duniya ta sa idanu sosai akan masu safarar makaman da baragurbin jamiái da masu safarar miyagun kwayoyi da kuma masu aikata manyan laifuka wadanda ke haddasa taása ta kashe kashen jamaá da haifar da rudani a tsakanin alúma.