KOFI ANAN YA AMINCEWA DA BUKATAR AMURKA DA IRAQI... | Siyasa | DW | 27.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

KOFI ANAN YA AMINCEWA DA BUKATAR AMURKA DA IRAQI...

Sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Anan ya amsa kiran da kasar iraqi da Amurka suka yi masa na sake tura jamian hukumar sa izuwa kasar ta iraqi don duba yiwuwa tare da taimakawa wajen gudanar da zabe na gama gari da yan kasar ta iraqi zasu mulki kansu da kansu. Kofi anan ya fadi hakan kuwa a yau talata a can birnin Paris tare da karin cewa hakan zai tabbata ne kawai idan sojojin hadaka a iraqi sun tabbatar da cewa akwai ingantaccen tsaro a cikin fadin kasar ta iraqi baki daya.

Bisa rahotanni da zarar jamian na mdd sun koma kasar ta iraqi zasu kalailaice yanayin dake faruwa ne a fadin kasar ta iraqi baki daya don duba yiwuwar gudanar da zabe kafin nan da 30 ga watan yuni na wan nan shekara da muke ciki. MDD dai a baya ta janye jami,an nata ne daga kasar ta iraqi a ranar 19 ga wata agusta na shekarar data gabata sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a babban ofishin ta dake birnin Bagadaza,wanda sakamakon hakan mutane 22 suka rugamu gidan gaskiya ciki har da jakadan majalisar na musanman a kasar ta iraqi.
Jim kadan dai bayan wadan nan kalamai na Anan sojojin taron dangi´bisa jagorancin kasar Amurka suka ce kalaman na Anan sunzo a dai dai lokacin da ake da bukatar su,domin a nasu ganin hakan zai taimaka wajen dankawa yan kasar ta iraqi mulkin su a hannun su ta hanyar gudanar da zabe a kasar.
Bisa hakan kuwa sojojin taron dangin sun tabbatar da cewa a nasu bangaren zasuyi duk iya bakin kokarin su na ganin an samu kwanciyar zaman lafiya a kasar ta iraqi don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu dangane da wan nan mataki da ake kokarin dauka. Bugu da kari a daya hannun kuma shugaban darikar shi,awa na kasar ta Iraqi Ali Al sistani ya tabbatar da cewa muddin jamian mdd suka gudanar da aikin su a kasar ta iraqi kamar yadda ya dace,kuma suka ce zabe ba zai yiwu ba to babu shakka zai amince da hakan shi da alummar sa baki daya.
A dai tun can baya ministan harkokin cikin gida dake cikin gwamnatin wucin gadi ta kasar,wanda dan kabilar shi,awa ne,wato Nuri Badran ya fada cewa gudanar da zabe a kasar ta iraqi a halin da ake ciki yanzu ba zai yiwuba a sabili da rashin tsaro da kuma rikice rikice dake faruwa a kai a kai.
A wata sabuwa kuma,duk da aiyukan kiyaye zaman lafiya da sojojin taron dangi keyi a kasar ta iraqi,har yanzu tashe tashen hankula naci gaba da gudana a yankuna daban daban na cikin kasar.
Na baya bayan nan kuwa shine na mutuwar wasu yan sandan kasar su bakwai,sakamakon musayar wuta da sukayi da yan fadan sari ka noke a ranar lahadin data gabata.
Sai kuma na rasa rayukan wasu sojojin Amurka biyu da farar hula daya da akayi sakamakon hatsarin da wani karamin jirgin saman na Amurka yayi a arewa da birnin Mosul.