Koffi Annan ya bukaci Amurika ta tura dakaru a yankin Darfur na kasar Sudan | Labarai | DW | 14.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koffi Annan ya bukaci Amurika ta tura dakaru a yankin Darfur na kasar Sudan

Sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia,Koffi Annan, ya yi kira ga shugaban Georges Bush, na Amurika da ya tura tawagar soja, ta mussaman, a yankin Darfur na kasar Sudan, domin kawo karshen rikicin wannan yanki, da ya ki ci, ya ki cenyewa.

Bayan ganawar da yayi da shugaba Bush, Annan ya fada wa manema cewa shugaban na Amurika na karbi shawara da hannu 2, saidai babu cikkaken bayyani, a game da ko ya amince, da aika dakarun, da yawan su da kuma lokacin aika su.

Ranar 3 ga watan februarun dam u ke ciki, komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, ya rattaba hannu akan kuri´ar amincewa da aika tawagar shiga tsakani ta Majalisar Dinkin Dunia a yankin Darfur, domin karfafa tawagar sojoji dubu 7 na kungiyar taraya Afrika.