1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ko yaya lamarin kasar iraqi ya kasance a yau

ibrahim saniMay 20, 2005

A yayin da ake kokarin tabbatuwar sabuwar gwamnati a iraqi a lokacin ne kuma ake ci gaba da fuskantar tashe tashen hankula

https://p.dw.com/p/Bvbo
Hoto: AP

Kamar kullum dai a yau ma an fuskanci tashin wani bom a kusa da wata tawagar soji a yankin kadhimiya na birnin Bagadaza,wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan sojin Iraqi biyu da kuma jikkata wasu guda uku.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayanin koda dai dasa bom din akayi ko kuma dan kunar bakin waje ne ya tashi bom din,to amma bincike kann hakan na nan naci gaba da gudana.

Jim kadan bayan faruwar hakan kuma wani bom din ya kara tashi a kudu masu gabashin Birnin na Bagadaza. Wan nan bom dai a cewar rahotanni anyi niyyar ya tashi da wata tawagar sojin Amurka ce dake wucewa to amma hakan bata samu ba,domin kuwa babu wanda ya rasa ransa ko kuma ya jikkata.

A yayin da ake cikin wan nan hali kuwa a waje daya da yywa daga cikin yan iraqi na cikin dari darin yadda lamarin sallar Juma,a ta yau zata kasance bisa la,akari da tashin bom din daya faru a jiya alhamis a yankin Saydiya wanda hakan ya salwantar da rayukan wasu masallata biyu da jikkata wasu guda biyar.

Idan kuma za a iya tunawa a karshen watan daya gabata wani dan kunar bakin wake ya tashi wani bom a kusa da masallacin yan shi,a dake Bagadaza a lokacin sallar Juma,a wanda hakan yayi sanadiyyar rayukan masallata guda tara tare da jikkata wasu kusan talatin.

A yanzu haka dai da yawa daga cikin shugabannin dariku na kasar sun dukufa kain da nain wajen janyo hankalin magoya bayan su dasu gujewa rikice rikice da tashe tashen hankula a tsakanin juna,domin a cewar su hakan na kara yamutsewar al,a murra a kasar yanzu haka.

A waje daya kuma karamin sakatare na harkokin wajen Amurka wato Robert Zoellick cewa yayi yan kunar bakin wake dana sari ka noke ne ke gudanar da aiyuka iri daban daban don ganin cewa an samu rarrabuwar kawuna a tsakanin kabilun kasar ta iraqi,wanda a ganin sa shine ummul aba,isin gaza samo bakin zaren tabbatuwar zaman lafiya a fadin kasar baki daya.

Idan dai za a iya tunawa a can baya an fuskanci rashin jituwa mai tsananin gaske a tsakanin manya manyan kabilu da kuma mabiya dariku iri daban daban na kasar ,wanda har yanzu ba a sami galabar shawo kann al,amarin ba.

A wata sabuwa kuma jim kadan bayan gudanar da sallar juma,ar yau da yawa daga cikin yan shi,a sun goggoge tafin kafafuwan su da tutucin Amurka dana israela kamar yadda mai tsattsauran raayin nan ya bukaci dasu yi.

Muqtadarr Al sadr ya dai bukaci yan darikar ta shi,a ne dasu gudanar da wan nan aiki a matsayin Allah wadai da Abin da akace ya faru a gidan yarin Guantanamo Bay dake kasar Cuba.

Idan dai za a iya tunawa a yan kwanakin baya ne jaridar Newsweek ta Amurka ta buga labarin cewa an wulakanta Al,qur,ani mai girma a yayin da ake tuhumar wasu daga cikin daurarru a gidan yarin,wanda hakan ya janyowa amurka Allah wadai daga kasashen musulmi na duniya daban daban.

To amma kuma a waje daya wan nan jarida tace wan nan labari data buga ba gaskiya bane domin kuwa akwai kura kurai a cikin sa.

A wata sabuwa kuma a yanzu haka sabon faraministan na iraqi wato Ibrahim Al Jafari ya iasa kasar Turkiyya don gudanar da wata ziyarar aiki.

Wannan dai itace ziyarar shugaban na farko a tun bayan darewar sa karagar mulkin kasar yan kwanaki kadan da suka gabata.

A dai lokacin wannan ziyara Ibrahim Al Jafari zai tattauna batutuwa ne da suka shafi tsaro da ciniki a tsakanin sa da shugabannin kasar.