Ko Karnuka suna gani a duhu | Amsoshin takardunku | DW | 20.11.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Ko Karnuka suna gani a duhu

Bayanin yadda karnuka suke gani da dare

Kare da Lasifikar DW

Kare da Lasifikar DW

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fitone daga hannun Malama Saadatu Atiku, Shagamu, Ogun, Najeriya. Malamar ta ce, Shin, Karnuka kuwa suna gani a cikin duhu?Muna musu ne ni da miji na, ko mu ringa kunnawa karenmu na gida fitila da dare ko kuwa a’a?

Amsa : To malama Saadatu, binciken da muka yi ya tabbatar mana da cewa , ke da mai-gidanki kun fi bukatar haske da dare fiye da karenku na gida. Amma dai don kada mu shiga share ba shanu, daga nan Bonn na tuntubi Dr Adamu Abubakar Yarima, Likitan dabbobi a Jihar Kadunan Tarayyar Najeriya, ga kuma tattaunawar da mukai da shi,game da amsar wannan tambaya.

Dr Yarima: E babu shakka kare yana gani a cikin duhu, kuma sabo Allah ya halicce shi domin ya rika gani cikin Kankanin haske sai ya yi masa baiwa ta cikakkaken gani koda kuwa a cikin duhu ne.Mafi kankantar hasken da Kare yake bukata domin gani , dai dai yake da kaso daya bisa shida na hasken da Mutum yake bukata domin gani.

Bashir: To likita yaya zaka kwatanta mana gani irin na mutane da gani irin na Karnuka?

Dr. Yarima: Ba kamar Idon mu na Yan-adam ba, su Karnuka Allah ya halicci Idonsu domin su rika gani a cikin dan kankanin haske. Ma fiya yawan Halittun Allah da suke da ido suna da wasu kwayoyin halittu guda biyu akan tantanin kwayar Ido da ake kira “retina’’ a turance. Kuma wadannan halittu guda biyu su suke taimakawa Ido wajen sarrafa haske, kuma ana kiransu da suna “Rods’’ da “Cones’’. Wadannan halittu guda biyu, sune suke sarrafa haske, su kuma sarrafa duk wani abu da Ido ya gani su aikawa da kwakwalwa domin tantancewa. Su Rods sun fi aiki sosai a haske mai dishi-dishi kuma sukan sa a ji motsin wani abu, yayin da su kuma Cones suka fi aiki a cikin haske sosai domin fayyace kala da kuma cikakken bayanin abinda Ido ya gani.

To shi Idon Kare wannan halitta ta Rods it ace ta mamaye shi, wanda hakan ya ba shi dammar gani a cikin haske mai dishi-dishi ko mai kankantar sa. Sannan kuma sukan taimaka musu wajen jin motsin wani

abu, wanda hakan ya sa suka zama dabbobi masu amfani wajen farauta.To amma kuma Karnuka suna da kimanin kashi daya ne daga cikin goma na Cones din da Mutum yake da shi, sabodahaka basa ganin kalar abu kamar yadda Mutum yake ganinsa.

Bashir: To ai likita bama batun kunnawa Kare fitila ba, anan Nahiyar Turai, wani bincike da aka gudanar a Kasar Ingila ya nuna cewa karnuka sun fi iyayen gidansu cin lafiyayyen abinci

Binciken da aka buga a watan Yuni, an gano cewa, Turawan Ingila suna ciyar da abokan nasu wato karnuka, mafi lafiyar abincin da su kansu ba sa iya ci.

Binciken wanda aka gudanar kan masu karnuka 1,337 ya gano cewa kashi 18 cikin 100 na wadanda aka gudanar da binciken kansu, suna shirya wa karnukan sabon abincin alfarma dauke da nama zuku-zuku fiye da wanda su suke ci, maimakon ba su abincin da aka ci aka rage.

Sannan kuma kashi 21 suna ba wa karnukan abin lasawar nan da ake kira da suna cizi (Chiese), yayin da kashi 15 ake ciyar da su kifi sannan kashi tara suke rayuwa kan kayan marmari irin na lambu.

Fiye da rubu’in wadanda aka tambaya sun ce suna cin irin abincin da suke saya wa karnukansu.

Binciken ya kuma ce a shekara Turawan Ingila suna biyan fam Miliyan dubu-biyu da 300 kimanin Naira 300 don shirya wa karnukansu dina (cin abincin dare).

 • Kwanan wata 20.11.2006
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvV9
 • Kwanan wata 20.11.2006
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvV9