1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko farfesun Kaza yana maganin Mura

Abba BashirFebruary 5, 2007

Bayani akan yadda farfesun kaza yake maganin Mura

https://p.dw.com/p/BvUz
Kaza da Kwai
Kaza da KwaiHoto: AP

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawar mu ta wannan makon,ta fito daga hannun mai sauraron mu a yau da kullum, Malam Adamu Ayyuba, Mazauni a garin Matamai da ke Jamhuriyar Niger. Malamin cewa yayi,“A likitance, menene gaskiyar batun da ake cewa,Farfesun kaza yana maganin cututtuka, musamman madai cutar Mura

Amsa: Dangane da wannan tambaya, na tuntubi Dr. Auwal Ibrahim Yola, Likita a asibitin cututtuka masu saurin yaduwa, dake Birnin Kano a Tarayyar Najeriya.Ga kuma abin da ya ce, game da amsar wannan tambaya

Dr. Yola: Wato bama farfesun kaza ba, ko da farfesu ne na kifi ko na Naman dabbobi irin su Rago da Shanu da dai sauransu, suna da amfani kwarai a jikin mara lafiya, musamman ma masu mura.Abin da yasa nace haka shine, shi farfesu cike yake da wani nau’i na sinadaran kayan abinci masu gina jiki wanda ake kira da Tutanci“Protein’’. Shi protein, shine yake dauke da sinadaran da suke gina jikin Dan-adam kuma su inganta shi,kuma yana dauke da wadansu sunadarai wadanda suke bunkasa garkuwar jikin Dan-adam.

Ga masu mura kuwa, kasancewar farfesu yana dauke da kayan yaji irin su, kanumfari da masoro da citta da barkono da dai sauransu, to wadannan kayan yaji kan taimaka kwarai da gaske wajen Bunkasa garkuwar jikin mai mura da kuma taimakawa jiki wajen fitar da majina. Shi yasa ko da yaushe a asibiti ake umartar marasa lafiya da su rinka amfani da irin wannan nau’in abinci domin saurin samun kuzari da lafiya

Ana bukatar farfesu ya kasance mai matsakaicin yaji,kada ran kada han,wato dai, dai-dai masali. Amma ga mutane masu lalurar da bata son yaji, irin su cutar alsa da sauransu to ba lailai suyi amfani da farfesu mai yaji ba.