1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya: Ziyarar Tebboune a Faransa

June 6, 2023

A cikin wannan wata na Yuni ne ake sa ran shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune zai ziyarci kasar Faransa, wacce ta yi wa kasarsa mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/4SFww
Aljeriya | Abdelmadjid Tebboune Faransa | Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da na Aljeriya Abdelmadjid TebbouneHoto: Ludovic Marin/AP/picture alliance

Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da dangantakar kasashen biyu ke ci gaba da fuskantar matsaloli. Har yanzu akwai sarkakiya da ke tattare da alaka tsakanin kasashen Aljeriya da Faransa, dangane da abubuwan da suka faru a baya da kuma matsalolin da suke kunno kai a yanzu. Hasali ma, a bazarar da ta gabata ne kasashen biyu suka sake warware wani babban rikicin da ke tsakaninsu. A watan Fabarairu ne, 'yar gwagwarmayar Aljeriya da ke rike da fasfo din Faransa Amira Bouraoui ta tsere daga Aljeriya zuwa Tunisiya, tare da taimakon hukumomin Faransa domin kaucewa dauri. Ita ce dai ta kafa kungiyar Barakat, domin nuna rashin amincewa da wa'adi na hudu na Shugaba Abdelaziz Bouteflika. A shekara ta 2021 an yanke mata hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari, kafin a sake ta watanni biyu bayan haka sakamakon afuwar da aka yi mata. Amma Amira Bouraoui ta tafi Faransa a 2023 lamarin da Aljeriya ke dauka a matsayin cin fuska ne daga bangaren Faransa, inda ta kira jakadanta domin nuna rashin amincewarta.

Karin Bayani: Aljeriya da Faransa na sa-in-sa tsakaninsu

A watan Maris Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da Abdelmadjid Tebboune sun tattauna ta wayar tarho domin guje wa "rashin fahimta, lamarin da ya sa a karshen watan Maris jakadan Aljeria ya koma bakin aikinsa. Amma ko da bayan batun Bouraoui dangantakar kasashen biyu na cikin mawuyacin hali, dangane da batutuwa masu mahimmanci. A baya-bayan nan ne dai wasu fitattun masana 'yan kasar Faransa suka rubuta budaddiyar wasika ga shugaban Aljeriyan, ta neman a sako dan jaridar nan Ihsane El Kadi da ke tsare a kasar. Majalisar dokoki ta kungiyar Tarayyar Turai ma na neman a sake shi, saboda haka ake ganin cewar da kamar wuya Shugaba Macron na Faransa ya iya yin watsi da wannan batu lokacin da zai gana da Shugaba Tebboune na Aljeriya. Zine Ghebouli na majalisar kula da huldar kasashen waje ta Turai ya ce, tsamin danganta tsakanin Aljeriya da Faransa na da dadadden tarihi.

Aljeriya | Algiers | Faraansa | Kwarangwal
Faransan ta mayar da kwarangwal din wasu 'yan Aljeriya da aka halaka a mulkin mallakaHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Doudou

Wani batu da ya dade yana jawo cece-kuce shi ne, tunawa da mulkin mallaka da Faransa ta yi wa Aljeriya daga 1830 zuwa 1962 wanda ya kai ga yakin Aljeriya. Har yanzu dai 'yan Aljeriya na jin haushin kalaman da Macron ya yi a watan Oktobar 2021, inda ya zargi yankin Maghreb na cewa Aljeriya ta ci gaba da yin amfani da laifin da Faransa ta aikata ta hanyar mulkin mallaka, domin biyan bukatunta na yau da kullum. A wannan marra ma, Aljeriya ta janye jakadanta a Faransa na tsawon watanni tare da hana jiragen sojojin Faransa yin shawagi a sararin samaniyarta. Sai dai masanin kimiyyar siyasa Zine Ghebouli na majalisar kula da huldar kasashen waje ta Turai ya ce duk da cece-kuce da bacin rai, ba za a iya kaucewa yin sulhu tsakanin Aljeriya da Faransa ba. A nata bangaren Faransa ta sanar da cewa za ta kara kyautata wa 'yan Aljeriya kusan dubu 200 da suka yi yaki a bangaren Faransa a yakin neman 'yancin kai, inda za ta biya su da iyalansu da zuriyarsu karin kudi. Da ma da yawa daga cikinsu na rayuwa cikin kangin talauci bayan da aka gama yakin, yayin da sababbin shugabanni suka yi musu kisan gill wasu kuma aka kai su Faransa bayan da suka yi nasarar tserewa.

Karin Bayani: Sabon rikici tsakanin Maroko da Aljeriya- Me ya sa rikicin ya ki ci ya ki cinyewa?

Sannan matakin da Faransa ta dauka na rage rabin adadin biza da ake bai wa 'yan Aljeriya, ya haifar da nakasu a dangantakar kasashen biyu. Fadar mulki ta Paris ta ce tana mayar da martani ne kan yadda kasashen Maghreb suka ki karbar 'yan kasarsu da Faransa ta kora, sai a watan Disambar bara ne gwamnatin ta Paris ta janye wannan takunkumi. A daya hannun kuma, Aljeriya ta dauki matakin dakile shige da fice ba bisa ka'ida ba. Dukkanin kasashen biyu na da sha'awar daidaita dangantakarsu, amma Maroko da ke zama abokiyar hamayyar Aljeriya na fargabar cewa kusanci tsakanin Faransa da Aljeriya na iya kawo cikas a rikicin yammacin Sahara. Don haka Maroko za ta iya amfani da matsalar bakin haure da ke neman tsalllakawa Turai ta barauniyar hanya, wajen rage tasirin Aljeriya a bangaren kula da kan iyaka.