1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Ko akwai mutanen dake zama a Sahara?

Ƙabilun dake gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum a yankunan Sahara.

default

Larabawan yankunan sahara.

Yanayin sahara dai, shi ne yankunan ƙasar dake fama da rashin ruwa. Sai dai, duk da haka, akwai ɗimbin mutanen dake gudanar da rayuwa da yin aiki, game da yin tafiye tafiye a irin waɗannan wuraren. Mutanen da suka fi shahara wajen gudanar da rayuwarsu a yankunan Sahara, sune Larabawa Makiyaya, waɗanda aka fi sani da Badwii - asalinsu sun fito ne daga yankunan larabawar dake yammacin hamadar sahara.

Galibi, waɗannan mutanen sukan yi ƙaura ne da dabbobinsu a cikin rairayin hamada domin samun wuraren da dabbobinsu zasu sami cimaka, sukan kuma yi amfani da Tantuna a matsayin wuraren kwana. A duk lokacin da suke yin tafiya - musamman da daddare, sukan yi la'akari da Taurari a matsayin jagora. Mutane daban daban ne ke zama a wuraren dake da ruwa da bishiyoyi a yankunan sahara da kuma yankunan tsaunukan dake da sanyi, kana ake yawaita samun ruwar sama. Mazauna yankunan sahara, inda ake samun ruwa da itatuwa sukan yi Noma, a yayin da sauran kuma ke yin kiwon dabbobin da suka haɗa da Tumaki da Shanu da kuma Rakumma.

Ɗaya daga cikin al'ummomin dake zaune a irin waɗannan yankuna, ita ce al'ummar Al-Kharija ko kuma Kharga dake ƙasar Masar. Yankunan tsaunukan kuwa, sun haɗa da tsaunukan Ahaggar dake kudancin ƙasar Algeria, da Tibesti Massif a arewacin ƙasar Chadi - inda al'ummar Toubou ko kuma Teba ke rayuwa a matsayin ɓurɓushin masu amfani da harshen mazauna saharar da suka yaɗu a Duniya.

A shekarun baya bayannan, fasahar zamani ta sanya wasu mutane gudanar da rayuwarsu a yankunan hamadar sahara. Daga cikin mazauna yankunan a yanzu, akwai Jami'ai, da 'yan kasuwa da kuma jikokin bayin da suka rayu a wuraren da suka zarta sahara - ciki harda ƙananan garuruwa kamar Tamanrasset a ƙasar Algeria. Manyan Tankoki ne a yanzu suka maye gurbin dabbobin da ake yin amfani dasu wajen gudanar da harkokin yau da kullum a irin waɗannan yankuna. Hakanan, akwai al'ummomin wannan zamanin da suka yi ƙaura zuwa yankunan saharar dake da ɗimbin arziƙin man fetur da iskar gas a ƙasashen Libya da Algeria.

Sai dai kuma sanin yawan mutanen dake rayuwa a yankunan sahara, abune dake da matuƙar wahala. Yankunan dai nada faɗi sosai, kana gashi gwamnatocin yankunan basu da isassun albarkatun ƙasa. Bugu da ƙari kuma, yawan ƙaura da makiyaya ke yi, sun sa da wuya a iya samun haƙiƙanin alƙalumar ƙididdigar jama'ar yankin. Amma duk da haka adadinsu yakai na miliyoyin mutane.

Mawallafi : Saleh Umar saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala