Klinsmann yayi murabus | Labarai | DW | 12.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Klinsmann yayi murabus

Mai horar da yan wasan kasa na jamus Jürgen Klinsman,ya sauka daga wannan matsayi nasa,bayan shekaru biyu yana horar da yan wasan na jamus.An tabbatar da murabus din Klinsman ne a taron manema labaru daya gudana a birnin Frankfurt.Yanzu haka dai mataimakinsa Joachim Löw,shine ya maye gurbinsa.An dai bukaci Mr Klinsman wanda ke da zama a kudancin califonia a kasar Amurka,daya cigaba a matsayin mai horar da yan wasan na kasa,bayan ya jagorancesu zuwa samun matsayi uku na uku a gasar cin kofin duniya da aka kammala a wannan makon.