Kitir-kitir na toshe mai a Amirka | Labarai | DW | 27.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kitir-kitir na toshe mai a Amirka

Kamfanin mai na BP wanda yake ta kitir-kitir don shawo kan man dake malala a tekun Miziko, yace akwai haske

default

Masu aikin ceto a tekun Mixiko

Kamfanin mai na BP yace yunƙurinsa na biyu, wajen toshe man dake tsiyaya a tekun Mexiko yana tafiya kamar yadda aka tsara, sai dai kamfanin yace suna buƙatar sa'o'i 24 kafin su tabbatar ko aikin mutum mutumin da aka sa ya yi a ƙarƙashin tekun ya samu nasara. Kamfanin dai yana son yin anfani da mutum mutumi, wanda zai ɗau laka ya maka a bakin bututun kafin ya sake maka siminti a kai, don tushe man dake tsiyaya. Wannan abune da ba'a taba gwadawa ba a ƙarƙashen teku mai zurfin mita 1600. A halinda ake ciki dai shugaba Obama yana fiskantar matsin lamba, inda kuma a jiya yace yana tunanin neman taimako daga waje, domin duk ketir ketir ɗin da BP ya yi, bai ci nasara ba. Aƙalla gallon miliyan 20 suka malala cikin teku, tun kwanaki 36 da yafara tsiyayewa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman  

Edita: Umaru Aliyu