1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kissan Hrant Dink

January 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuTz
Kisan gillar da aka yi wa wani dan jaridar Turkiyya dan usulin Armeniya Hrant Dink ya haddasa Allah waddai da tofin Allah tsine daga sassa daban daban na duniya. Jamus, mai shugabancin Kungiyar Tarayyar Turai a halin yanzu haka ta bayyana kaduwarta da wannan kisa. Wasu ‚yan bindiga da ba’a san ko su wane ne ba, sunka bindige dan jaridar a wajen shelkwatar jaridar tasa dake birnin Istanbul, abun da ya haddasa zanga-zangar dubban mutane. Rahotanni sun ce mahukuntan kasar Turkiyya na fuskantar mutane masu tarin yawa da tambayoyi. Kungiyoyin kare hakkin dan-Adam da gwamnatin Armeniya sun dora wa gwamnatin Turkiyya wani bangare na alhakin wannan danyyen aiki saboda gazawar da tayi wajen bai wa Hrant Dink cikakkiyar kariya duk da barazanar kisan kai da yake fuskanta. Dan jaridar ya harzuka masu tsananin kishin kasa a Turkiyya dangane da ra’ayinsa akan kisan kiyashin da aka yi wa Armeniyawa a karkashin daular Usmaniya ta Turkiyya tsakanin 1915 zuwa 1918. A ranar talata ne za a yi jana’izarsa