1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

October 3, 2009

Kisan kiyashi da sojojin Guinea suka yiwa ´yan zanga-zanga shi ya fi ɗaukar hankalin jaridun na Jamus

https://p.dw.com/p/Jx7f
Hoto: AP

A wannan makon kisan kiyashin da aka fuskanta a ƙasar Guinea shi ne babban abin da ya fi ɗaukar hankalin jaridun Jamus. A lokacin da take ba da rahoto akan wannan ta'asa jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Sojojin ƙasar Guinea dake mulki sun ɗauki wani tsattsauran mataki na murƙushe yunƙurin al'umar ƙasar na ƙirƙiro wata manufa ta adawar farar fula. Alƙaluma na kafofi masu zaman kansu sun ce sama da mutane metan aka kashe a wani mataki na zub da jini da sojojin Guinea suka ɗauka inda suka shiga harbin kan mai uwa da wabi domin tarwatsa masu zanga-zangar adawa a Konakry babban birnin ƙasar. Wannan mataki da gwamnatin soja ta ɗauka zai iya haddasa mayar da ƙasar saniyar ware a dangantakar ƙasa-da-ƙasa."

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung sai da ta tofa albarkacin bakinta akan wannan mummunar ta'asa a rahoton da ta bayar ƙarƙashin taken:"Harbe-harbe akan mutanen da basu san hawa ba ba su san sauka ba." Jaridar ta ce:

Moussa Daddis Camara Machthaber Guinea
Moussa Daddis Camara, shugaban gwamnatin mulkin sojin GuineaHoto: dpa

"Tun bayan ɗarewarsa kan karagar mulki a wajejen ƙarshen shekarar da ta wuce, shugaban gwamnatin sojan ƙasar Guinea Moussa Camara yake famar cika baki game da yaƙar cin hanci a ƙasar. Amma fa kawo yanzun ba wani abin da faru. Kuma matakin da sojojin suka ɗauka yana mai yin nuni ne da irin tsoron dake tattare a zuciyar shugaban a game da kifar da gwamnatinsa. Wani abin takaici ma shi ne yadda sojojin ke ci gaba da tsunduma cikin gari don wawason ganima."

Ƙasar China, kamar yadda rahotanni suka nunar, tana da niyyar zuba maƙudan kuɗi a Nijeriya a ƙoƙarinta na cin gajiyar arziƙin man fetur da Alla ya fuwace wa ƙasar. Jaridar Die Tageszeitung tayi nazari akan haka inda take cewa:

"Bayanai sun nuna cewar a halin yanzu haka kamfanin CNOOC, kamfanin mai mafi girma a ƙasar China na tattaunawa da gwamnatin Nijeriya domin sayen kashi ɗaya cikin shida na rijiyoyin man ƙasar ta yammacin Afurka akan zunzurutun kuɗi dala miliyan dubu 30. In hakan ta tabbata to wannan cinikin shi ne zai kasance mafi girma irinsa da China ta taɓa gudanarwa a Afirka. Chinar na fatan cin gajiyar manufofin gwamnatin Nijeriya ne a game da mayar da wasu ɓangarori na kamfanonin manta a hannun 'yan kasuwa masu zaman kansu. To sai dai kuma kawo yanzu majalisar dokokin ƙasar na hana ruwa gudu game da wanzar da wata dokar da ta tanadi wannan manufa."

Deutschland gegen Südafrika in Leverkusen
Philipp Lahm, na Jamus a dama da Bernard Parker na Afirka Ta Kudu a huguHoto: AP

Yanzun dai watanni kaɗan suka rage kafin a gabatar da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya a Afirka ta Kudu. To sai dai kuma har yau ana fama da tababa game da al'amuran tsaro a ƙasar. Jaridar Die Welt tayi gabatar da rahoto akan haka tana mai cewa:

"Alƙaluma sun nuna ƙaruwar yawan farmaki a kantuna da gidajen mutane da misalin kashi 42 cikin ɗari. Kuma ko da yake an samu raguwar yawan kashe-kashe na gilla da misalin kashi uku cikin ɗari, amma fa har yau akan kashe mutane kimanin 50 a rana, lamarin da ya sanya Afirka ta Kudun ta zarce kowace ƙasa ta duniyar nan yawan kashe-kashe na gilla."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal