Kisan kare dangi a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 01.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisan kare dangi a Sudan ta Kudu

Hukumar kare hakin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana aikata kisan tsabtace kabila a Sudan ta Kudu.

Südsudan Flüchtlinge (picture-alliance/AP Photo/S. Wandera)

Yara da mata da tsofaffi suka fi fuskantar kisan gilla

Shugabar hukumar kare hakin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu Yasmin Sooka ta fada a cikin wata sanarwa cewa an aikata ko kuma ana ci gaba da aikata kisan tsabtace kabila a wasu yankuna na kasar abinda ke nuni da yiwuwar maimaita irin kisan kiyashi da ya auku a kasar Ruwanda a 1994, lokacin da aka kashe mutane kimanin dubu 800. Jami'ar ta nunar da haka ne a karshen ziyarar kwanaki 10 a Sudan ta Kudu. Ta ce matsananciyar yunwa da yi wa mata fyade cikin gungu da kone kauyuka sun zama ruwan dare a wasu yankuna na kasar. Sai dai shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya musanta zargin na MDD yana mai cewa babu irin wannan abu na kisan tsabtace kabila a Sudan ta Kudu. Kasar dai ta shafe kusan duk tsawon gajeren tarihinta cikin yakin basasa. A shekarar 2011 ta samu 'yancin kai amma gaba tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa ta kunno kai a karshen 2013, abinda ya haddasa rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa.