1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan jama'a ya ƙaru a Afganistan a shekarar bara

Abdourahamane HassaneFebruary 14, 2016

Wani rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana ya nuna cewar shekara da ta wuce ta 2015 ta kasance mafi zubar da jini al'umma a Afganistan.

https://p.dw.com/p/1HvGt
Bildergalerie Kinder und Krieg in Afghanistan
Hoto: Getty Images/AFP/S. Marai

Rahoton ya ce an kashe mutane dubu 11 a yaƙin da ake yi a ƙasar a shekarar,addadin da ya zarta na shekara ta 2014 da kishi huɗu cikin ɗari. Ɗaya cikin mutum huɗu wanda faɗan ya ritsa da shi, yaro ne, sannan akwai kamar kishi 37 na mata da lamarin ya shafa.

Danielle Bell ita ce daraktan kula da kare hakkin ɗan adam na Majalisar ta Ɗinkin Duniya. ''Ƙaruwan kisan da kishi huɗu yana da nasaba ne da ƙarin harin ƙunar baƙin wake da 'yan Taliban ke kai wa a Kabul da kuma Kunduz. Rundunar sojojin ƙasar ta Afganistan da kuma 'yan sanda ba su da ƙarfin tinkarar mayaƙan Ƙungiyar Taliban.Tun bayan ficewar dakarun ƙawance na ƙasashen duniya daga Afganistan ɗin a shekara ta 2014.