1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

080709 Ägypterin Mord

Tijani LawalJuly 9, 2009

A ranar Laraba ta makon jiya wani Bajamushe haifaffen ƙasar Rasha kashe wata Bamasariya har lahira lokacin shari'a a wata kotu dake birnin Dresden.

https://p.dw.com/p/IkZw
Dubunnan mutanen da suka halarci jana'izar Marwa El SherbinyHoto: dpa


Bajamushen haifaffen Rasha ya daɓa wa bamasariyar mai suna Marwa El-Sherbini wuƙa ne inda hakan yai sanadiyar mutuwarta har lahira lokacin shari'a a wata kotu, wai saboda ƙarar da ta ɗaukaka kansa sakamakon cin mutuncinta da ya yi. Matar mai juna biyu da ke da shekaru 32 na haifuwa a birnin Alexnadariya dake Masar. Wannan kisan gilla ya harzuƙa jama'a, ba ma a nan Jamus kaɗai ba har da sauran ƙasashe, musamman na larabawa.

A dai halin da ake ciki yanzun ba wani jami'in siyasar Jamus dake sha'awar tsayawa madadin Bernd Erbel, jakadan Jamus a kasar Masar, wanda ala-tilas yayi taro da manema labarai domin Allah Waddai da wannan ɗanyyen aiki. An saurara daga bakinsa yana mai cewar:

Erbel ya ce: A daidai wannan lokaci na baƙin ciki ina fatan tabbatar muku da cewar illahirin al'umar Jamus na Allah waddai da wannan ɗanyyen aiki kuma kotu za ta yi dukkan iyawarta don tantance gaskiyar lamarin."

Abin nufi a nan shi ne kotun zata gabatar da hukunci mai tsanani akan mai laifin kisan, wanda tuni yake tsare a hannun mahukunta, wanda kuma aka ce kafin ya aikata ɗanyyen aikin nasa sai da ya riƙa gabatar da wasu kalamai na ƙyamar baƙi da nuna goyan bayansa ga jam'iyyar nan mai neman sake ra'ayin Hitler ta NPD a zauren kotun.

A can ƙasar Masar dai mutane na tattare da imanin cewar mahukunta Jamus gaba ɗaya sun yi wa lamarin riƙon sakainar kashi. Jaridar Al-Masry Al Yaoum ta ce abin lura a nan shi ne ba wani jami'in siyasar Jamus da ya nuna ƙarfin zuciyar halartar zaman makokin Marwa El-Sherbini a birnin Berlin, a yayinda ita kuma Al-Aharam ke cewa wannan ba wani mataki ne na ɗaiɗaikun mutane ba, wata alama ce ta adawa da Musulmi kuma gwamnatin Jamus ce ke da alhakin tabbatar da tsaro a kotunan ƙasar. A lokacin da yake furta ta bakinsa Tarik El-Sherbini ɗan uwan matar da aka yi wa kisan gillar cewa ya yi:

"Na je Jamus ranar juma'ar da ta wuce. Daga wajen abokan arziƙinmu a Jamus muka samu labarin abin da ya faru, ba daga ofishin jakadanci ko mahukuntan ƙasar ba. Mahukuntan ma ba su labarta wa ofishin jakadancin ba. Gaba ɗaya ana rufa-rufa a lamarin saboda ba wanda ya faɗa mana sunan alƙalin ko ɗan sandan da lamarin ya shafa."

A dai halin da ake ciki yanzun ofishin ɗaukaka ƙara na gwamnati na shawarar gabatar da ƙara akan wani ɗan sandan da aka ce ya buɗe wuta nan take kan mijin El-Sherbani wai a zatonsa shi ne mai alhakin harin. Tuni kuma gwamnati ta musunta zargin da ake mata na sako-sako da lamarin inda wakiliyar gwamnati akan al'amuran baƙi Maria Böhmer ta fito fili tayi Allah waddai ta ɗanyyen aikin ta kuma miƙa gaisuwar ta'aziyyarta ga mijin El-Sherbani.

A kuma halin da ake ciki sakatare-janar na majalisar Yahudawan Jamus ya Stephen Kramer da takwaransa na majalisar Musulmin ƙasar Aiman Mazyek sun kai wa mijin El-Sherbi dake kwance a asibiti ziyara, inda Kramer ya ce wajibi ne a samu haɗin kai don tinkarar wannan cin mutuncin ɗan-Adam da ake yi ba ƙaƙƙautawa.