Kisan gilla akan Ahmad Kadyrov | Siyasa | DW | 10.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kisan gilla akan Ahmad Kadyrov

A jiya lahadi aka kai hari tare da halaka shugaban Chech´niya Ahmad Kadyrov a lokacin wani faretin sojan da aka shirya a babban filin wasa na Grozny domin bikin tunawa da nasarar da Sojan Tarayyar Soviet suka samu a yakin duniya na biyu

Hoton marigayi Ahmad Kadyrov

Hoton marigayi Ahmad Kadyrov

A daidai lokacin da ake biki da murna a shagulgulan da aka kira wai na nasara, sai ga shi murnar shugaban Rasha Vladmir Putin ta koma ciki. A daidai wannan rana, inda kusan a dukkan birane da garuruwan Rasha ake jerin gwano da faretin soja domin bikin nasarar da sojojin kasar suka samu a yakin duniya na biyu, ‚yan tawayen Chechniya suka halaka hakimin da fadar mulki ta Kremlin ta nada domin tafiyar da al’amuran wannan lardi. Shugaba Ahmad Kadyrov, wanda ya sha tsallake rijiya da baya a yunkure-yunkuren kisan gillar da ake yi masa, a jiya lahadi ya hadu da ajalinsa, inda ya rasu sakamakon munanan raunukan da ya samu. Magoya-bayan Kadyrov da sojojin Rasha sun lashi takobin shan fansa. Amma fa wadannan matakai na ramuwar gayya ko kadan ba zasu taimaka a shawo kan matsalar Chechniya ba. A maimakon haka ma tashe-tashen hankulan lardin zasu dada yin tsamari ta yadda da wuya a samu zaman lafiya. A dai wannan marra da muke ciki yanzun Chechniya ta zama tamkar wani tabo ne ga kasar Rasha kuma dandalin kashe-kashe da wahalhalu ga masu aikin sojan bauta wa kasa. Ita kanta fadar mulkin Chechniya ta Grozny tuni ta zama kango sakamakon yakin da yayi kaca-kaca da ita. Dukkan kudin da Rasha take bayarwa domin sake gina birnin suna kwarara ne zuwa aljifan janarorin sojan kasar dake jan akalar yakin. Magoya bayan marigayi Ahmad Kadyrow sun sha zargin kungiyoyin kare hakkin dan-Adam da laifukan wawason kudaden taimako. Babban shaida a game da wannan korafi kuwa shi ne kasancewar ‚yan gidaje kalilan ne ake sake gigginawa a garuruwa da kauyukan Chechniya, a yayinda dubban daruruwan mutane ke ci gaba da zama a sansanonin ‚yan gudun hijira da aka tanadar musu. An yi shekara da shekaru fadar mulki ta Kremlin tana mai kiyawa kememe game da ba wa ‚yan jarida daga kasashen yammaci wata dama ta kai ziyarar gane wa idanuwansu abin dake faruwa a lardin na Chechniya. Dalili kuwa shi ne tsoron da take yi ka da martabar shugaba Putin ta zube a idanun duniya. A zaben da aka gudanar a lardin a cikin watan oktoban bara alkaluma sun ba wa marigayi Ahmad Kadyrov rinjayen kashi 80% na jumullar kuri’un da aka kada. Amma fa zaben bai tafi akan wata hanya madaidaiciya ba, saboda shugaba Putin ya dauki matakai na tsoratar da duk wani dan takarar da ka iya zama kalubala ga mutumin da ya nada ta yadda ala-tilas suka janye daga zaben. A dai ‚yan watannin da suka wuce Kadyrov yayi bakin kokarinsa wajen samar da wata ‚yar kwarya-kwaryar kwanciyar hankali a lardin Chechniya, inda ya sanya aka rika farautar abokan adawarsa da kuma ‚yan aware, ba sani ba sabo, sannan a daya bangaren ya ware wasu kudade na tukuici ga wadanda suka dawo daga rakiyar ra’ayinsu na ta da kayar baya. To sai dai kuma da yawa daga ‚yan tawayen sun yi amfani da wannan dama suka karbe ‚yan kudadensu ba tare da sun nuna biyayya ga shugaban ba, wannan kuma shi ne abin da ya ba da kafar cimma nasarar makarkashiyar kisan gillar da aka yi masa. A yanzun dai ba wanda ya san yadda al’amura zasu kasance nan gaba. Putin, ba shakka, zai nemi wani sabon hakimin da zai rike masa lardin Chechniya, mai yiwuwa ta hanyar sabon zabe. Amma a hakika wannan rikici sai tare da taimako daga ketare ne za a iya shawo kansa.