Kisan gilla a Afganistan | Labarai | DW | 08.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisan gilla a Afganistan

Ƙasashen duniya sun yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa masu aikin agaji a Afganistan.

default

Yankin Nuristan a Afghanistan

An kama direban motar turawan da aka hallaka ranar juma'a a Afganinsta. 'Yan sanda sukace an kama shine don gudanar da bincike, kan mutuwar turawa takwas da 'yan Afganistan biyu, waɗanda ke aikin agajia a ƙasar. Ga dai abinda matar ɗaya daga cikin Amirkawa shida waɗanda aka hallaka ɗin take cewa" Na kaɗu ko da yaushe muna tare da shi, wannan karon ban bi shi ba, sabo da ɗiyar mu tana da jariri a hannu. Ya sadaukar dukkan rayuwansa wajen samarwa 'yan Afganistan kiwon lafiya, kuma za'a binne shi ne a maƙabatar kristoci dake can a birnin Kabul. Ƙungiyar Taliban ta ɗauki alhakin kisan mutane, wanda tace 'yan leƙen asirine da kuma yaɗa addinin kirista". Yanzu haka dai ƙasashen duniya sun fara mai da martani, in sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton tace wannan kisan na dabbanci ne, yayin da ita kuwa ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International, tace wannan shine kisan gilla mafi muni a Afganistan da akayiwa masu bada agaji. A wani labarin da ya shafi Afganistan, an kashe wasu dakarun NATO guda biyar a kudancin ƙasar. Sanarwar tace biyu daga cikin sojojin da aka kashen Amirkawa ne. Tudan farko dai gwamnatin Denmark tace itama an kashe mata sojojoji biyu a jiya asabar, lokacin da motar da suke ciki ta taka bam a kudancin lardin Helmand.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Muhammed Abubakar