1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisan bajamushe a Afghanistan

Wani bajamushe ya rasa ransa a harin ƙunar bakin wake da ake kai a ƙaddamar a Afghanistan.

default

Dakarun Jamus a Afghanistan

Wani bajamushe ya rasa ransa a Afghanistan a lokacin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam da ke jikinsa a cibiyar raya ƙasa ta Amirka da ke arewacin ƙasar. Wasu ƙarin mutane 11 sun ji rauni a wannan harin da ya wakana a birnin Kunduz. Gwamnan lardin na Kunduz, wato Mohammad Umar ya ce, an yi nasarar kashe wasu ƙarin 'yan ƙunar bakin waken biyu kafin su tayar da bam da ke jikinsu.

Tuni dai 'yan taliban suka ɗauki alhakin wannan harin.Cibiyoyin ƙungiyon Amirka a Afghnistan na daga cikin inda 'yan taliban suka fi kai hare-hare tun bayan ƙazantar fito na fito tsakanin dakarun ƙawance da Amirka ke jagoranta da kuma masu tsananin kishin addini.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Halimatu Abbas