Kirkiro gidan Radio da kuma na’urar kallo ta DVD | Sauyi a Afirka | DW | 27.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Kirkiro gidan Radio da kuma na’urar kallo ta DVD

Muhammad Hadi Usman wani ne da Allah ya hore masa basira ta kirkirar na’urori dabam-dabam irin su DVD da ma na’urar sauraron maganganu daga nesa.


Shi dai Muhammad Hadi Usman ko kuma Injiniya Hadi, kamar yadda aka fi sanin sa, Allah ya huwace ma sa basira ta kirkirar naurori dabam- dabam ta hanyar amfani da abubuwa na gargajiya da na zamani duk da cewa bai taba shiga ko da ajin firamare don yin karatun Boko ba. Banda gidan Radiyo da ya kirkira da kuma gidan talbijin, yanzu haka ya hade wannan naura inda ta kunshi DVD da ma naurar sauraron maganganu daga kusurwoyi dabam-dabam da kuma dan karamin gidan radiyo mai zuwa mita 300 a takaice.


Dukkanin naurorin nan dai ya kirkire su ne cikin wata kwarya da ya yi wa lakabi da "Tummude Hadi". Banda wadan nan naurori, Injiya Hadi ya na shirin samar da naurar da za ta dauko hotunan abubuwan da mutane ke yi daga nesa. Injiya Hadi ya bayyana cewa indan zai samu tallafai daga gwamnati ko Kungiyoyi masu zaman kan su musamman na dakin bincike, to zai iya kirkirar naurori da za su taimaki alumma tare da samar da ayyuka ga daruruwan matasa.


Yanzu haka dai akwai matasa da dama da suka samu aiki sanadiyyar zama da Injiya Hadi kuma manazarta akan abubuwan yau kullum sun yi imanin cewa irin su Injiya Hadi na bukatar tallafi daga gwamnatoci a dukkanin matakai domin su samu damar baje basirar su don amfanin alumma, sannan wasu na ganin cewa ya kamata gwamnati ta samar wa wannan bawan Allah dakin bincike tare da hada shi da masana domin tatsar irin basirar da Allah ya huwace masa don amfanin alumma.