1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiraye-kirayen rusa kamfanin mai na Najeriya

Uwais Abubakar Idris/ASAugust 6, 2015

Kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa sun bayyana bukatar rusa daukacin kamfanin kula da harkokin man fetir na Najeriya NNPC wanda ke fuskantar muhimman sauye-sauye.

https://p.dw.com/p/1GBIW
Shell Bonny Island Öl Umweltverschmutzung Niger River Delta in Nigeria
Hoto: Getty Images

Kungiyoyin kare hakin jama'a dai sun yi gaba wajen yin cara a kan sauye-sauyen da ke faruwa a kamfani NNPC mai kula da harkokin man fetir na Najeriya wanda ya yi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa. Abinda ya sanya su bayyana cewa canji da ake fuskanta abu ne da aka dade ana jiran ganin faruwarsa, amma fa a sonsu a rusa tsarin don sake lale.

Auwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar CISLAC da ke yaki da cin hanci a Najeriyar na daga cikin masu son ganin an rusa kamfanin inda ya ke cewar ''babban dalilinmu shi ne idan har gyara ba zai yiwu ba a a NNPC, ba amfani barinsa a haka, muddin za'a ci gaba da cin hanci da rashawa to gara ma a ruguza shi. Ba zai yiwu ba a ce NNPC ne ke yin hada-hada ba kuma shi ke sa ido kana shi ne ma mai yin doka. Wannan shi ya kawo cin hanci da rahswa a kamafanin.''

Futurando 24 - Öl in Nigeria
Rashin kula da wuraren tonon mai ya sanya malar mai a yankuna da dama a Najeriya.Hoto: DW

Wannan kira na kungiyoyin na zuwa ne dai lokacin da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya salami manyan daraktocin kamfanin guda takwasa tare da rage yawansu zuwa guda hudu a sabbin zubi da aka nada, abinda ke zaman 'yar manuniyar ta irin manyan sauye-sauye na ban mamaki ga ga kamfanin.

Tuni dai hantar daukacin ma'akatan kamfanin na NNPC ta kada sakamakon wannan guguwa ta sauyi da ke kadawa, wacce ka iya yin awan gaba da duk wanda ke da guntun kashi na cin hanci da rashawa. Wannan sabon yanayi da aka shiga ya sanya mutane irinsu Barrister Mainasar Umar mai sharhi a kan al'ammuran yau da kullum a Najeriya hango haske ga yadda aka faro gyara a kasar.

Nigeria Benzin Schwarzmarkt
Cin hanci da rashawa na daga cikin abubuwan da ke haifar da karanci mai.Hoto: picture-alliance/dpa/T. Owolabi

To sai dai ra'ayoyi sun sha bamban a kan nauyi ko ma tsarin gyaran da ake gunadawar a wannan sashi. Mr Ezenwa Nwagu da ke jagorantar wata kungiya ta fara hula, ya ce ''maganar rusawa magana ce ta matsawa da kosawa na samun canji, amma idan har mutane suka nuna kishin kasa za'a samun canji, ai ba tsarin ne yake da matsala ba, jama'a ne da ke ciki suke da ita.''