1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kirar MDD game da kwalara a Haiti

November 12, 2010

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Haiti na bukatar makudan kuɗaɗe wajen daƙile cutar amai da gudawa da ta ɓarke.

https://p.dw.com/p/Q7a6
Yaran da ke fama da kwalara a HaitiHoto: AP

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a kai wa ƙasar Haiti ɗaukin kimanin miliyon 120 na Euro, domin ta samu damar daƙile cutar amai da gudawa da ta ɓarke tun kwanaki baya. A lokacin wani taron manaima labarai da ta gudanar a birnin Geneva, mai magana da yawun hukumar da ke kula da ayyukan jin ƙai ta majalisar wato Elisabeth Birs ta ce akwai bukatar agaza wa Haiti cikin gaggawa da magunguna da likitoci da kuma ruwa mai tsafta, matiƙar ana son hana yaɗuwar cutar ta kwalera a faɗin ƙasar.

Alƙaluman da ma'aikatar kiwon lafiyar ƙasar ta wallafa a shafinta na Internet sun nunar da cewa mutane 724 ne cutar ta amai da gudawa ta hallaka ya zuwa yanzu a ƙasar ta Haiti. Yayin da wasu ƙarin mutane 11.000 ke ƙwance a asibiti don samun magani. Hukumomin lafiya sun yi hasashen cewa mutane aƙalla miliyon guda da dubu 300 na cikin barazanar kamuwa da cutar ta kwallara a Port-au-Price babban birni da sauran sassan ƙasar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu