Kiran saban shugaba Nigeria ga al´ummar ƙasa. | Labarai | DW | 24.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kiran saban shugaba Nigeria ga al´ummar ƙasa.

Saban shugaban ƙasar Nigeria, AL haji Musa Er Aduwa, ya gabatar da wani ɗan ƙwarya- ƙwaryan jawabi, a cibiyar jam´iyar PDP dake birnin Abuja.

Shugaban ƙasa, ya yi kira ga al´ummomin Nigeria su kwantar da hankulla su kuma duƙƙufa wajen aiyyukan ci gaban ƙasa.

A halin yanzu a cewar sa, yaƙin neman zaɓe ya ƙare, lokaci yayi na haɗa ƙarfi da ƙarfe, na dukkan yan Nigeria domin hidda surfe daga ruwa.

Ranar 29 ga watan da mu ke ciki ne, Umaru Musa Yar Aduwa, zai hau karagar mulki, domin maye gurbin Olesegun Obasanjo.