Kira game da ′yan adawan Bama | Labarai | DW | 18.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kira game da 'yan adawan Bama

Ban Ki-Moon da Aung San Suu Kyi sun nemi hukumomin sojan Bama su sake 'yan adawan ƙasar

default

Jagorar adawa ta Bama Aung San Suu Kyi

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon da kuma madigar 'yan adawan Bama Aung San Suu Kyi sun yi kira ga hukumomin sojan ƙasar da su sake ɗaruruwan 'yan adawa da ke tsare. A lokacin da suka tattauna ta wayar taraho, Ban Ki-Moon da kuma Aung San Suu Kyi sun nuna bukatar da ke akwai na sake 'yan adawa a matakin sulhunta ɓangarorin da ke gaba da juna, tare da neman girka dauwamammiyar demokuraɗiyya.

Kakakin babban magatakardan na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya sanar da haka ya ce Ban Ki-Moon ya jadadda matsayin hukumar da yake shugabanta ga Suu Kyi game da yunƙurinta na sadaukar da kai domin ci gaban ƙasarta. Shekaru bakwai ita Aung San Suu Kyi da ta taɓa lashe lambar yabo ta Nobel, ta shafe ta na shan ɗaurin talala a hannun hukumomin mulkin sojan ƙasarta.

A jimilce dai shekaru 15 cir Suu Kyi mai shekaru 67 ta shafe a ɗaure a shekaru 20 na baya-bayannan na gwagwarmayar samar da cikakken 'yanci da walwala ga 'yan ƙasarta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal