Kira ga dage zaben shugaban kasa a Burundi
July 6, 2015Talla
Shugabannin ƙasashen gabashin Afirka sun yi kira da a ɗage zaɓen shugaban ƙasar Burundi har ya zuwa ranar 30 ga wannan wata na Yuli da muke ciki.Sun bayyana haka ne a lokacin wani taron koli da ƙungiyar ƙasahen gabashin Afirka ta shirya a yau a ƙasar Tanzaniya a wani yinƙuri na neman shawo kan rikicin siyasar ƙasar Burundi.
Sai dai mafi yawancin shugabannin ƙasashen yankin ba su halarci taron ba wanda shugaban ƙasar ta Tanzaniya da takwaransa na ƙasar Yuganda ka dai suka halarta,a yayin da Shugaba Paul Kagame na ƙasar Ruwanda da Uhuru Kenyatta na ƙasar Kenya dama Pierre N'Kurunziza na ƙasar ta Burundi suka wakilto wasu ministocinsu kawai zuwa taron.