Kimanin kamfanoni 6700 daga kasashe 111 ne ke halartar bikin baje kolin litattafai na bana a Frankfurt | Siyasa | DW | 06.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kimanin kamfanoni 6700 daga kasashe 111 ne ke halartar bikin baje kolin litattafai na bana a Frankfurt

Bikin baje kolin litattafai na kasa da kasa a birnin Frankfurt, bana zai mayar da hankalinsa ne ga dangantaka da huldodin al'adu na kasashen Larabawa

Shugaban gwamnati Gerhard Schröder na gabatar da jawabin bude bikin baje litattafai

Shugaban gwamnati Gerhard Schröder na gabatar da jawabin bude bikin baje litattafai

Da yawa daga mawallafa na kasashen Larabawa dake zaman hijira a ketare sun yi korafin cewar dandalin baje kolin litattafan wani fage ne na taka rawar farfaganda, saboda yawa-yawancin marubuta adabi dake halartar zauren masu biyayya ne ga manufofin gwamnatocin kasashensu. Amma Volker Neumann, darektan hukumar shirya bikin baje kolin litattafan ya musunta wannan zargi, inda ya ce ko da yake kasashen Larabawan da ake karbar bakuncinsu a dandalin bikin su ne ke daukar nauyin hada-hadarsu ta irin litattafan da zasu baje, amma tun da farkon fari aka gayyaci sauran mawallafa, wadanda ba a kaunar ganinsu a kasashensu. Volker Neumann ya kara da bayani yana mai cewar:

Wani abu mai muhimmanci shi ne gayyatar mawallafa, wadanda ke sukan lamirin manufofin gwamnatocin kasashensu kuma Ibrahim Al-Moallem, shugaban gamayyar madabi'un Larabawa, wanda shi kansa mai goyan bayan manufar fadin albarkacin baki ne, ya taimaka wajen ganin an cimma nasarar haka. Ita gamayyar ta gidajen litattafan Larabawa, kungiyar ce mai zaman kanta kuma ba ta da wata alaka da gwamnati.

A halin da ake ciki yanzu haka da yawa daga masu korafin sun canza ra’ayoyinsu, abun da ya hada har da marubucin adabin nan na kasar Masar Nagib Mahfuz mai lambar yabo ta Nobel, wanda ya rubuta wani jawabi na bude bikin kolin litattafan na Frankfurt. An dai lura da yadda batutuwa na siyasa suka dabaibaye bikin na bana a cikin jawabin da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya bayar yana mai fatali da ikirarin nan da ake yi na rashin jituwar al’adu tsakanin al’ummomi a sassa dabam-dabam na duniya. Schröder ya ce a zamanin baya akan la’anci Musulmi ba tare da wata basira ba. A saboda haka a ganinsa wannan biki na baje kolin litattafai zai taimaka a kawo karshen wannan batan basira a kuma bude wani sabon babi na musayar yawu da fahimtar juna. Schröder ya kara da cewar:

A duk inda aka samu hulda ta gaskiya da fahimta da kuma hakuri da juna to kuwa annamimanci ba zai samu wata kafa ta kawo baraka tsakanin kasashen Larabawa da na yammacin Turai ba.

Kasashen Larabawan dake halartar dandalin bikin zasu yi bakin kokarinsu wajen wayar da kan jama’a a game da yanayin al’adunsu a fannoni na rayuwa da zamantakewar jama’a da rubuce-rubuce na adabi da harkoki na siyasa, wadanda suka saba da labaran nan na dare dubu da daya.