Kimamin ´yan yawon bude ido 20 aka yi garkuwa da su a Ethiopia | Labarai | DW | 03.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kimamin ´yan yawon bude ido 20 aka yi garkuwa da su a Ethiopia

Hukumomi a kasar Ethiopia sun ce sun yi imani baki kimanin 20 ne aka yi garkuwa da su a wani yankin karkara na kasar inda ´yan tawaye suka kafa sansani. Tun a ranar laraba ´yan yawon bude ido da suka hada da ´yan kasar Faransa 10 da kuma wasu mutane 10 daga kasashe dabam dabam suka bata a lokacin da suke ziyartar yankin Afar dake can arewa maso gabashin Ethiopia. Sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Margaret Beckett ta tabbatar da cewa ma´aikata biyar na ofishin jakadancin Birtaniya a Addis Ababa na daga cikin mutanen da suka bata. A cikin shekarun baya-bayan nan yankin na Afar ya kasance wata cibiyar garkuwa da ´yan yawon bude ido.