1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kifi mafi Girma a Duniya

Abba BashirNovember 14, 2006

kifi mafi girma da aka taba kamawa a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVA
Whale Shark
Whale SharkHoto: AP

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fitone daga hannun Malam Aminu Iliya, Argungu, Kebbi, Najeriya.Malamin ya ce, abokina ya ce, a Argungu ne aka kama kifi mafi girma a duk cikin kifayen da aka taba kamawa a Duniya, ni kuma na musanta hakan. Da fatan zaku warware mana musun da muke yi, ta hanyar sanar da mu kifi mafi girma da aka taba kamawa a Duniya, da kuma wurin da aka kama shi?

Amsa: Bincike ya tabbatar mana da cewa , wani Kifi da ake kira da suna Whale shark a Turance,shine kifi mafi girma da aka taba kamawa a Duniya. Wato a Hausance dai a iya bayyana wannan kifi da cewa, babban Kifin da ake samu a Teku. Kuma an kama wannan Kifi ne a Tekun Kasar Thailand, a shekarar 1919, wato kimanin shekaru 87 kenan da suka wuce. Tsawon wannan Kifi dai ya kai kafa 59, kuma ba wai gamdakatar akai ba, dama dai shi jinsin kifi na Whale shark, shine jinsin kifi da aka dauka a matsayin kifi mafi girma a Duniya, inda bisa al’ada babban kifi na Whale shark yakan kai tsawon kafa 45 , a nauyi kuwa yakan kai har Ton 15, wato kimanin buhu hatsi 150 kenan.

An fara gano kifin Whale shark a watan Afrilun 1828, lokacin da aka gudanar da wani bincike a dakin bincike na kimiyya akan wani karamin Whale shark da ka kama , wanda tsawonsa ya kai kafa 15 a Kasar South Africa. Kuma daga baya an samu cikaken bayanin wannan kifi daga wani likitan sojoji mai suna Andrew Smith, tare da taimakon wasu Sojoji ‘Yan Kasar Birtaniya wadan da suka yi kaka-gida a birnin Cape-town, inda a shekarar 1849 aka radawa wannan kifi suna Whale shark. Kuma ya samu wannan suna ne saboda tsananin girmansa da kuma yanayin cin abincinsa. Gashi dai Shark ne, amma mai girma da yanayin cin abinci Irin na Whale.

Ana samun nau’i na irin kifin Whale shark a Tekunan da suke a bangaren Kasashen Duniya masu zafi.ko da dai, bincike da aka yi na kimiyyar halittun ruwa na baya-bayannan, ya tabbatar da cewa, yawansu yana raguwa.