Kidayar jamaá a Nigeria | Labarai | DW | 22.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kidayar jamaá a Nigeria

A yau aka shiga rana ta biyu ta ƙidayar jamaá a Nigeria. Hukumomi a fadin ƙasar sun ɗauki tsauraran matakai na taƙaita zurga zurgar jamaá a yayin ƙidayar tare da buƙatar jamaá su zauna a gidajen su domin a ƙidaya su. Shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo yace maƙasudin ƙidayar ita ce tabbatar da adadin yan Nigeria, sabanin wasu tunani da zarge zarge da wasu ɓangarorin jamaá ke yi. ƙidaya ta ƙarshe da aka gudanar a Nigeria it ace ta shekarar 1999 wadda ta baiyana yawan alúmar Nigeria a kan mutane miliyan 89.9