1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kibaki yaƙi amincewa da dokar tauye aikin yan Jarida

August 23, 2007
https://p.dw.com/p/BuDR

Shugaban ƙasar Kenya Mwai Kibaki ya ƙi sanya hannu akan wata doka da aka yi ta Allah wadai da ita wadda ke da nufin tauye kafofin yaɗa labarai. Mr Kibaki yace dokar ta yi karan tsaye ga ribar dimokraɗiyar da ƙasar ta samu a baya bayan nan, yana mai cewa zai mayar da dokar ga majalisar dokoki. Da shugaban ya amince da dokar, to da zata baiwa kotuna damar tilastawa yan jarida faɗin salsalar labaran su. A makon da ya gabata ɗaruruwan yan jaridar Kenya suka yi gangami a kofar Majalisar dokokin ƙasar domin baiyana adawar su da daftarin dokar.