Khatami yayi Allah wadan harin 9/11 | Labarai | DW | 11.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Khatami yayi Allah wadan harin 9/11

Tsohon shugaba kasar Iraki Mohammed Khatami yayi Allah wadan kungiyar Alqaeda ta osama bin laden,kana a hannu guda kuma ya yabawa kungiyoyi kamar na Hizbollah saboda kalubalantar halayyan mulkin mallaka da danniya na Izraela.A jawabin mintuna 30 daya gabatar a jamiar Harvard a jiya lahadi,tsohon shugaban Iran Khatami ya sake maimaita yabonda wa ingantuwan democradiyya,sai dai yace yan siyasar Amurka tun bayan yakin duniya na biyu sun mamaye harkokin siyasar duniya.Mohammed Khatami yace yana daya daga cikin shugabanin kasashen duniya na wancan lokaci da sukayi Allah wadan harin kunar bakin waken daya ritsa da Amurka a 2001.

 • Kwanan wata 11.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5U
 • Kwanan wata 11.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5U