1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KHAN YA SAIDAWA IRAN,LIBYA DA K/AREWA SIRRIN MAKAMAI

ZAINAB AM ABUBAKARFebruary 3, 2004
https://p.dw.com/p/Bvm6
A ranar Asaba din nan ne aka sallami Sanannen masanin kimiyan nan na Pakistan Abdul Qadeer Khan,daga mukaminsa na na mai bawa prime minista shawara,saboda kasancewa babban wanda ake zargi da laifin binciken daya dauki watanni biyuz yana gudana,dangane da zargin cewa wasu yan Pakistan din sun mikawa wasu kasashe sirrin makamakan Nuclearn data mallaka.
Bugu da kari yanzu haka ana binciken wasu manyan jamian gwamnati 7,to sai dai manyan jamian Soji da masu leken asiri,da kwararru sukayi nuni dacewa suna sane da Harkokin Khan,baa gurfanar dasu ba domin bincike.
A hannu guda kuma gurfanar da Khan gaban kotu zai zame babban barazana wa Pakistan,inda ake masa kallon jarumihn kasa kana wanda ya kirkiro Atom Bomb bana pakistan kadai ba amma a duniyar musulmi baki daya.Wani babbabn jammin Sojin kasar yace Khan ya amince da bawa wadannan kasashen uku sirrin yin makamaia karshen shekarun 1980 zuwa farkon 1990.To sai dai babu tabbaci dangane da gurfanar dashi gaban hukuma. Majiyar hukumar leken asirin Pakistan ta tabbatar da wannan zargi da akewa Khan,wadanda kuma sun isa a gurfanar dashi gaban hukuma,ciki harda da rahoto daga wani mutumin Dubai dake shiga tsakani a wannan harka.Bugu da kari zaayi danganta wannan zargi da yadda yake tafi da rayuwarsa.
To sai dai Jamian diplomasiyya na kasashen yammaci da masu lura da alamura dakaje suzo,na ganin cewa gurfanar dashi gaban hukuma zai zame tonon silili wa Pakistan,musamman Sojin ta wadda keda karfi a wannan kasa.
A hannu guda kuma jamian leken asirin kasar na zargin cewa mai yiwuwa yar wanda ake zargin ta tafi kasar waje da wasu shaidu da iya kasancewa tonon asiri wa sojin kasar.A halin yanzu dai,ana lura da alamuran Khan mai shekaru 69 da haihuwa,kuma tun da aka fara wannan binciken baice uffan ba a bainar jamaa.
A watanni biyu da suka gabata ne Pakistan ta fara binciken wannan batu,bayan da hukumar lura da makamashi ta duniya ta sanar da samun shaida dake nuni dacewa Pakistan nada hannu cikin harkokin makamashin Nuclearn Iran.Bugu da kari akwai tabbacin cewa kasashen Libya da Koriya ta arewa ma sunyi amfani da wadannan sinadaren da suka fito daga Pakistan.A dangane da hakane alummomin kasashen duniya ke fatan cewa gurfanar massu laifi makamancin wannan zai taimaka matuka gaya wajen kare yaduwar fasahar kera makamai masu guba a doran kasa,ayayinda a halin yanzu duniya na figirce dangane yiwuwan fadawan fasahar kera makamai hannun yan taadda.