Khamenei ya gargadi ′yan majalisar Iran | Labarai | DW | 28.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Khamenei ya gargadi 'yan majalisar Iran

Babban jagoran koli na addinin Islama na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bukaci sababbin 'yan majalisar dokokin kasar da aka rantsar da su yi taka tsan-tsan da kasashen yamma.

Ta cikin wani sako da ya aika wa sababbin 'yan majalisar, jagoran ya ce yanayin tsarin kasa da addini da kuma yadda al'umomin kasa da kasa ke kallon su cike da barazana yasha ban-ban da yadda kasar take ada. Ayatollah Ali Khamenei wanda shi ne ke yanke hukunci na karshe ga dukkan wasu muhiman batutuwa da suka tunkaro a kasar, ya kuma kara jaddada kiransa daya saba na ci gaba da yin biyayya ga dukkan tanade-tanden dokokin juyin-juya hali na shekara ta 1979 gami da nuna tirjiya ga dukkan wasu bakin al'adu na kasashen yammacin duniya.