Khalid al-Barnawi ya shiga hannu | Labarai | DW | 04.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Khalid al-Barnawi ya shiga hannu

Kungiyar 'yan ta'adda ta Ansaru mai goyon bayan kungiyar Al-Qaida na cikin tsaka mai yuwa bayan kame shugaban kungiyar a birnin Lokoja na jihar Kogi a Najeriya.

Jami'an tsaron Najeriya ne dai suka kama babban shugaban wannan kungiya mai suna Khalid al-Barnawi da ke zaman daya daga cikin gaggan 'yan ta'addan da kasar Amirka ke nema ruwa jallo. Shi dai Al-Barnawi dan shekaru 47 da haihuwa wanda kuma sunansa na ainihi shi ne Usman Umar Abubakar, ya kasance a sahun gaba na jerin sunayan 'yan ta'addan da jami'an tsaron na Najeriya ke nema. An dai kama shi ne a binin Lokoja na jihar Kogi a cewar mai magana da yawun rundunar sojojin na Najeriya Brigediya Janar Rabe Abubakar.

A shekara ta 2012 ne dai wani bangare na kungiyar Boko Haram ya kafa kungiyar ta Ansaru sakamakon rishin jituwa da ta kunno kai tsakanin Abubakar Shekau da shi al-Barnawi dan asalin garin Biu a jihar Borno wanda ya samu horo na ayyukan ta'addanci a kasashen Afghanistan da kuma Algeriya.