Kere-keren nakasassu a Najeriya | Sauyi a Afirka | DW | 22.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Kere-keren nakasassu a Najeriya

Wani mai nakasa a Nigeria ya kafa wata cibiyar nakasassu bisa kere-keren zamani dan horar da ‘yan uwansa kirar zamani, domin koya masu kananan sana'o'i.

Wani Gurgu mai kishin ‘yan uwansa matasa guragu kafa cibiya domin kawar da masu nakasa tunanin nan ta dabi'ar barace-barace a cikin zukatansu.

Mallam Isiyaku Musa Ma'aji shi ne shugaban ma'aikatar da ke bayyana cewa saboda kishin ‘yan uwansa ne ta sanya shi kirkiro wannan ma'aikata domin tabbatar da ganin cewa ya janyo hankalin su wajen yin bankwana da sana'ar barace-barace dan kama sana'ar da za ta ceci rayuwarsu a nan gaba,inda ya ce tun shekara sama da 20 ne suka kirkiro wannan ma'aikatar, kuma ya zuwa wannan lokacin, an samu damar ragowar yawar kananan yara mabarata da ke yawo a kan titunan garin Kaduna.

Babu shakka kere-keren gargajiya da na zamani duk ake koya wadannan matasa guragu a wannan cibiya, domin dai tabbatar da ganin cewa sun koya suna kuma fafatawa da sauran matasa masu kira a cikin gari da ke sana'ar kere-kere, da zummar rage yawan matasa guragu mabarata.